Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nikki Haley Za Ta Yi Murabus


Nikki Haley

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley ta ba da Amurkawa mamaki bayan da kwatsam ta bayyana shirinta na yin murabus. Kodayake ta gaya ma Shugaba Trump tun watanni shida da su ka gabata.

Ba zato ba tsammani jakadiyar Amurka a Majaisar Dinkin Duniya, Nikki Haley, ta bayyana cewa za ta yi murabus a karshen wannan shekara ta 2018. Nikki Haley, wadda tuni ta mika takardar yin murabus dinta ga Shugaba Donald Trump, wanda shi kuma ya amince, ta ce ba za ta yi takara a 2020 ba. Hasali ma, za ta taya Trump yakin neman zabe a 2020 din. To sai dai ba yi bayyana musabbabin yin murabus din ba.

A martaninsa kan al’amarin, Shugaba Trump ya ce Nikki Haley ta yi aiki tukuru a Amurka da kuma duniya baki daya.

Nikki Haley ta ce ta gaya ma Shugaba Trump tun watanni shida da su ka gabata cewa za ta yi murabus zuwa karshen wannan shekarar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG