Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nkurunziza Ba Zai Halarci Taron Tanzania Ba


Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza

Rahotanni daga Burundi na cewa shugaban kasar Pierre Nkurunziza, ba zai halarci taron kolin shugabannin kasashen yankin gabashin Afrika ba, wanda zai tattauna kan rikicin siyasar kasarsa.

Taron kolin, zai gudana ne a Dar es Salaam, zai kuma samu halartar shugaban kasar Uganda, da na Tanzania da na Kenya, kana Rwanda za ta tura minista ya wakilce ta, yayin da ita Burundin za ta tura Ministan harkokin wajenta.

Kakakin shugaba Nkurunziza, Gervais Abayeho, ya gayawa Muryar Amurka cewa, shugaban ya maida hankalinsa ne kan yakin neman zabe, inda ya kara da cewa shugaban ya makara a yakin neman zaben, saboda halartar taron da ya gabata, wanda aka yi yunkurin yi mai juyin mulki.

Wannan yunkuri da Shugaba Nkurunziza ke yi na neman yi na tazarce ya haifar da mummunar zanga zanga, wadda ta lakume rayukan mutane 20 a irin arangamar da ‘yan sanda ke yi da masu bore.

A farkon wannan wata ne, masu adawa da shugaban na Burundi, suka yi yunkurin yin juyin mulkin da bai yi nasara ba, a lokacin yana halartar taron kolin kasashen yankin wanda ya tattauna kan kasar ta Burundi.

XS
SM
MD
LG