Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NNPC: Shugaba Buhari Ya Nada Sabon Babban Darakta


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Kamfanin Ma'akatar Man Fetur din Najeriya ko NNPC ya samu sabon shugaba

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya nada Dr Emmanuel Ibe Kachikwu a matsayin babban darakta na kamfanin man fetur din Najeriya da aka sani da NNPC a takaice.

Kafin a nadashi kan wannan sabon mukamin Dr Kachikwu wanda dan asalin jihar Delta ne shi ne mataimakin shugaban kamfanin man Exxon-Mobil shiyar firka.

Yayi karatun lauya a jami'ar Najeriya dake Nsukka a kudu maso gabashin kasar. Ya nada digiri na biyu da digirgir daga jami'ar Harvard dake nan Amurka.

Dr Kachikwu ya fara aiki ne da bakin kasuwanci da aka sani da suna Nigerian/American Merchant Bank.

Daga bankin ya koma kamfain Texaco inda ya yi aiki na tsawon shekara takwas.

Bayan shekarun da yayi a Texaco Dr Kachikwu ya samu aiki da kamfanin Exxon-Mobil daga inda Shugaba Buhari ya tsamoshi ya shugabanci NNPC.

XS
SM
MD
LG