Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NNPC Ya Yi Karin Bayani Kan Samun Sinadarin Mathanol A Cikn Man Fetur Da Aka Shigo Da Shi Najeriya


Mele Kolo Kyari

Shugaban kamfanin kasuwancin man fetur na Najeriya wato NNPC, Mal. Mele Kyari, ya yi karin bayani a game da yadda aka shigo da gurbataccen man fetur mai sinadarin Methanol da ya wuce kima daga kasar Belgium ba tare da an gano shi ba da kuma kamfanonin da suka shigo da shi.

Mal. Kyari ya bayyana cewa ba a gano sinadarin Methanol din a cikin man fetur din da aka fi sani da PMS a turance ba saboda a aikin tantance ingancin man fetur din babu batun tantance kaso na sinadarin Methanol a ciki.

Shugaban na kamfanin man fetur na Najeriya ya bayyana hakan ne da maraicen ranar laraba a wani taron manema labarai da ya gudana a birnin tarayya Abuja inda ya ce wannan matsalar dai ta haifar da karancin man fetur da kuma fuskantan dogon layukan a biranen Abuja, Legas, da kuma wasu jihohi da dama.

A cewarsa, wasu ‘yan kasuwa hudu ne suka shigo da gurbataccen man mai sinadarin methanol da yawan gaske cikin kasar daga birnin Antwerp da ke kasar Belgium.

Jami’an binciken ingancin man fetur dai sun gaza gano yawan sinadarin Methanol da ke cikin man da farko a wajen shigo da shi a kasar Belgium da kuma inda ake shigowa da shi a gabar tekun Najeriya saboda tun farko babu gwajin gano sinadarin na methanol a cikin aikin tantancewar saboda ba abunda aka saba yi bane sakamakon yadda bukatar sinadarin kadan ne a aikin.

Mal. Kyari ya kara da cewa, ka'idojin binciken ingancin man fetur kafin a fara fitarwa daga cikin jiragen ruwa da aka saba amfani da su a tashar lodin kaya a kasar Belgium da tashoshin fitar da su zuwa cikin Najeriya ba su hada da gwajin yawan sinadarin methanol ba saboda haka masu binciken ingancin kamfanin NNPC da hukumar kula da ingancin man fetur na NMDPRA ba su gano yapan sinadarin ba.

Shugaban na NNPC dai bai tabbatar da ranar da aka shigo da gurbataccen man cikin kasar ba amma ya bayyana cewa NNPC ta gano lamarin a karshen watan Janairun data gabata ne.

Ya bayyana cewa, ranar 20 ga watan Janairun shekarar 2022 kamfanin NNPC ya sami rahoto daga babban jami’in tantance ingancin man fetur kan kasancewar wasu ababe da aka jdanganta da emulsion a turance cikin man fetur da aka shigo da shi kasa daga birnin Antwerp na kasar Belgium, in ji Mal. Kyari.

Baya ga hakan akwai sinadarin Methanol a cikin jiragen dakon mai guda hudu in ji Mele Kyari.

Kyari ya ce kamfanonin da suka shigo da man cikin Najeriya sun hada da kamfanin MRS, Emadeb/Hyde/AY Maikifi/Brittania-U Consortium, Oando, da kuma kamfanin Duke.

Haka kuma, kamfanin MRS ya yi amfani da jirgin MT Bow Pioneer, kamfanin Emadeb/Hyde/AY Maikifi/Brittaniya-U Consortium ya shigo da samfurin man ta jirgin ruwa MT Tom Hilde; kamfanin Oando ya yi amfani da jirgin MT Elka Apollon, yayin da kamfanin mai na Duke ya shigo da mai ta hanyar amfani da jirgin MT Nord Gainer.

Kamfanin NNPC ya jadada cewa ba a gano sinadarin Methanol cikin man ba ta hanyar da aka saba tantance inganci domin tantance ingancin ba ya hada da kaso na Methanol.

Kyari ya kara da cewa takardun ingancin kaya da aka bayar a tashar lodin kaya na birnin Antwerp a kasar Belgium ta AmSpec Belgium sun nuna cewa man fetur din ya bi ka’idojin da Najeriya ta shimfida.

Kazalika, masu duba ingancin mai na kamfanin NNPC da suka hada da GMO, SGS, GeoChem da kuma G&G sun yi gwaje-gwaje kafin a sallame su, sun kuma nuna cewa man fetur din ya cika ka’idojin da Najeriya ta gindaya tun farko.

A cewar Mal. Kyari, a bisa ka’idar da aka saba bi a kan duk wani nau'in shigo da man fetur cikin Najeriya, an ba da takardar shaidar jigilar kayayyaki daidai da ingancin da aka sharudda daga wakilin da hukumar kula da dokoki ingancin da gidajen man fetur ta najeriya wato NMDPRA ta cika sharuddan Najeriya.

Yana da mahimmanci a lura da cewa ka'idojin binciken ingancin da aka saba amfani da su a cikin tashar jiragen ruwa na Belgium da kuma tashoshin fitar da su a Najeriya ba su hada da gwajin adadin methanol na kashi daya ba don haka masu binciken ingancin NNPC da NMDPRA ba su gano abin da aka kara na sinadarin methanol ba, in ji kamfanin NNPC.

Mal. Kyari ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa kamfanin NNPC na kara neman hanyoyin samun karin shigowa da mai cikin kasar domin biyan bukatun yan kasar na samun wadataccen man fetur.

Haka kuma kamfani NNPC ya yi tanadin dakile ci gaba da kai gurbataccen man fetur da aka samu cikin kasar tare da bada umarnin kebe duk wani man da ba a fitar da shi ba tare da hana tafiya da duk wanda abin ya shafa dake kan hanyar kaiwa gidajen mai.

Shugaban kamfanin NNPC ya sanar tare da yi wa kamfanonin da su ka shigo da kayan tun farko gargadi don gyarawa kuma kamfanin NNPC zai yi aiki da sauran masu ruwa da tsaki ciki har da hukumar kula da harkokin man fetur na kasar wato NMDPRA don kara daukar matakan da suka dace daidai da ka’idojin kasa.

Idan ana iya tunawa, da maraicen ranar Talata ne hukumar NMDPRA mai kula da inganci da gidajen man fetur na kasar ta tabbatar da samun gurbataccen mai cikin kasar ta kuma bukaci yan kasa su kwantar da hankulansu don masu ruwa da tsaki na daukan matakan da suka dace.

XS
SM
MD
LG