Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NNPP Ta Zabi Kwankwaso A Matsayin Dan Takararta A Zaben Shugaban Kasa


Tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso
Tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso

Kwankwaso wanda da mamba ne a jam'iyyar PDP da APC, ya ce ya san raunin dukkan ‘yan takarar kuma ba ya shakkar gamuwa da su ranar zabe.

Sabuwar jam’iyyar hamayya ta NNPP ta ayyana tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasa da za a yi a 2023.

Wannan ya nuna Kwankwaso zai tunkari ‘yan takarar manyan jam’iyyun da su ka hada da APC mai mulki da babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Tuni wasu jam’iyyun su ka gudanar da zaben fitar gwani kamar PDP da ta zabi Atiku Abubakar, Labor ta tsayar da tsohon gwamnan Anambra Peter Obi, inda APC za ta yi zabenta a ranar Litinin mai zuwa don shirin mika sunayen gwanaye ga hukumar zabe zuwa 9 ga watan Yunin nan.

Shugaban jam’iyyar NNPP Farfesa Rufa’i Ahmed Alkali ya ce sun yi dogon nazari kafin tsayar da Kwankwaso don ya zama daidai da sauran manyan ‘yan takara da za su fafata a zaben.

Kwankwaso wanda da mamba ne a jam'iyyar PDP da APC, ya ce yi wa dukkan ‘yan takarar farin sani kuma ba ya shakkar gamuwa da su ranar zabe.

Ya kara da cewa, NNPP za ta kawo wani tsarin da zai kawar da muradun ‘yan jari hujja a dimokrdaiyyar Najeriya.

Saurari cikakken rahoton Hauwa Umar:

NNPP Ta Zabi Kwankwaso A Matsayin Dan Takararta A Zaben Shugaban Kasa - 2'27"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00

XS
SM
MD
LG