Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Na Shirin Komawa APC Kuma Ba Ma Tattaunawar Sulhu Da Ganduje – Kwankwaso


Kwankwaso, hagu da gwamna Ganduje, dama (Facebook/Abubakar Aminu Ibrahim)
Kwankwaso, hagu da gwamna Ganduje, dama (Facebook/Abubakar Aminu Ibrahim)

Dangane da jita-jitar da ke cewa ana sulhu tsakaninsa da gwamna Ganduje, tsohon gwamnan na Kanon ya ce babu wani abu kamar haka.

Tsohon gwamnan jihar Kanon Najeriya Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce, ba shi da shirin komawa jam’iyyar APC ko wata jam’iyya kamar yadda ake ta rade-radi.

Cikin wata hira da ya yi da Channels TV a ranar Lahadi, tsohon ministan tsaron ya ce babu kamshin gaskiya a rahotonnnin da ke nuna cewa yana shirin sauya sheka.

“Babu wani shiri da nake yi na barin PDP na koma APC ko wata jam’iyya.” Kwankwaso ya ce.

Kwankwaso ya kara da cewa, a tashi fahimtar, abin da ya sa ake yada jita-jitar shirin barin shi PDP na da nasaba da babban taron da jam’iyyar ta yi a Kaduna na shiyyar arewa maso yammaci a watan Afrilun bara.

“Mun yi babban taronmu a watan Afrilun bara a Kaduna, inda na ga ba a yi min adalci ba, magoya bayana ma a arewa maso yammaci da sauran sassan kasar su ma suka ga kamar ba a yi mana da Kano adalci ba, hakan ya sa mutane suke cewa za mu bar PDP, wannan shi ne mafarin batun.” Kwankwaso ya fadawa mai gabatarwa Seun Akinbaloye a shirin Politics Today na Channels TV.

Dangane da jita-jitar da ke cewa ana sulhu tsakaninsa da gwamna Ganduje, tsohon gwamnan na Kanon ya ce babu wani abu kamar haka.

A cewar Kwankwaso, mutane sun yi amfani da ziyarar ta’aziyyar da gwamnan ya kai mai ne suka fara rade-radin cewa an fara sulhu.

“Tun daga 2015 da ya zama gwamnan Kano mutane ba sa ganinsa a gidana amma a wannan karon sai ya yanke shawarar ya zo.” In ji Kwankwaso.

Kwankwaso ya kara da cewa, ya ji dadin ziyarar da gwamnan ya kai masa saboda, “mu mun aminta da siyasar zaman lafiya da ci gaban Kano da kasa baki daya, amma baya ga haka (wannan ziyara) babu wata tattaunawa da ake yi.”

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG