Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NPFL: Karawar Kano Pillar Da Enugu Rangers, Sauran Wasanni


'Yan wasan Kano Pillars (Hoto: Shafin Instagram, Kano Pillars)

Gasar Premier League ta NPFL a Najeriya ta shiga zagaye na 14 a kakar wasa ta 2020/2021 yayin da Kwara United ke jagorantar teburin gasar.

Yayin da aka shiga zagaye na 14 a gasar cin kofin ta Premier a Najeriya NPFL a wannan karshen, kungiyar Kano Pillars za ta gwada kaiminta da Enugu Rangers.

Baya ga wannan wasa, za a a buga wasanni a sassa daban na kasar da suka hada da karawar Adamawa United da Dakkada Uyo.

Katsina United kuma za ta gwada sa’arta akan ‘yan wasan Sunshine Stars Akure na jihar Ondo yayin da da Nasarawa United za ta karbi bakuncin Lobi Stars ta Makurdi.

Ita kuwa Plateau United bakuncin MFM Legas za ta karba a daidai lokacin da Jigawa Golden Stars za ta kara da Rivers United.

A gefe guda kuma Warri Wolves za ta gwada kaiminta da Akwa United ta birnin Uyo sannan Wikki Tourist su kara da Kwara United.

A halin da ake ciki Kwara United ce ke saman teburin gasar da maki 25 Eyimba da ke rike da kofin gasar tana da maki 24 yayin da Enugu Rangers da Kano Pillars kowannensu ke da maki 23-3 amma Rangers na gaba da yawan kwallaye.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG