Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nuhu Ribadu Ya Raka ‘Yarsa Fatima Gidan Mijinta


Malam Nuhu Ribadu da 'yarsa Fatima (Hoto: @NuhuRibadu Twitter)

Tsohon shugaban hukumar da ke yaki da cin da rashawa a Najeriya EFCC, Malam Nuhu Ribadu, ya raka ‘yarsa Fatima dakin mijinta bayan da aka kammala shagulgulan biki.

A karshen makon nan aka daura auren Fatima da Aliyu Atiku, da ga tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.

“Yanzu na sauke ‘yata Fatima a sabon gidanta. Abu ne mai matukar sosa rai ga mahaifi idan ya zo sauke wannan nauyi.” Ribadu ya ce a shafinsa na Twitter.

A sakon nasa Ribadu, wanda ya taba tsayawa takarar shugaban kasa, ya kuma mika godiyarsa ga daukacin wadanda suka yi tururuwar zuwa bikin auren.

“Ina mai matukar nuna godiya ga wadanda suka halarci bikin da irin karamci da aka nunawa iyalina da wadanda suka aika sakon fatan alheri da addu’o’i.” Ribadu ya kara da cewa.

Auren, wanda aka daura a Abuja babban birnin Najeriya, ya samu halartar manyan shugabannin kasar, irinsu tsohon gwamnan jihar Legas Bola Ahmed Tinubu, tsohon gwamnan Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da gwamna mai ci a jihar Yobe Mai Mala Buni da dai sauransu.

Facebook Forum

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG