Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama na Matsa Lamba Akan Rasha


Shugaba Obama a Malaysia.
Shugaba Obama a Malaysia.

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce dole Amurka da Turai su hada guyawunsu, wajen kakaba ma Rasha jerin takunkumi, saboda matakan da ta ke daukawa a Ukraine, wadanda ya ce su na barazana ga 'yanci da kuma diyaucin kasar.

Shugaba Obama, yayin da ya ke jawabi a yau dinnan Lahadi a Malaysia, yace dole ne Amurka da Turai su dau matakan bai daya, su nuna ma Rasha cewa duniya fa ta yi mawafaka wajen kakaba takunkumin.

Mr. Obama ya ce sai da aka cimma yarjajjeniyar kwantar da kurar da Rasha, amma Rashar ta ki ta ko daga yatsa don shawa kan lamarin.

A jiya Asabar Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ya bukaci hadin kan Rasha ba tare da wani sharadi ba, game da bukutar sakin masu sa ido na Turai da mayakan sa kai magoya bayan Rasha su ka sace su ranar Jumma'a a gabashin Ukraine.

Wani babban jami'in Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ya ce Kerry ya gabatar da bukatarsa ta wayar tarho ga takwaransa na Rasha Sergei Lavrov. Daga bisani Rasha ta ce ta na daukar abin da ta kira "dukkannin matakai na warware matsalar," to amma ta dora ma Ukraine laifin kasa kare tawagar.
XS
SM
MD
LG