Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha da Ukraine Sun Tara Kayan Yaki a Iyakokinsu


​Firayim ministan Ukraine Arseniy Yatsenyuk na zargin Rasha da yunkurin mamaye Ukraine da karfin soji, da a siyasance, a dai-dai lokacin da kasashen guda biyu suka tara sojojin yaki a bakin iyakar dake tsakaninsu.

Mr. Yatsenyuk Juma’arnan yayi gargadin cewa matakan da Rasha take dauka zasu iya kaiga barkewar yaki a nahiyar Turai. Yayi wadannan kalaman ne a lokacin da yake tattaunawa da mambobin gwamnatinsa na rikon kwarya, inda ma yake cewa Rasha na so ta fara yakin duniya na uku.

Shugaban Amurka Barack Obama shima ya soki abunda ya kira cigaba da dagula lamura a gabashin Ukraine, wajenda ‘yan aware masu goyon bayan Rashe dake dauke da makamai suka mamaye ofisoshin gwamnati.

Da yake magana a birnin Seoul dake Koriya ta Kudu, Mr. Obama yace zai tattauna da muhimman shuwagabannin Turai a yammacin yau Juma’a, akan karawa Rasha takunkunmi, idan har Rashan ta cigaba da irin wadannan halaye nata a Ukraine.

Shugaba Obaman ya kara da cewa dole ne Shugaba Vladimir Putin ya yanke shawara idan yanaso ya ga tattalin arzikin kasarshi mara karfi ya kara lalacewa, saboda yaki bin hanyoyin diflomasiyya wajen warware takkadamar Ukraine.

Kalaman nashi sun zo bai daya ne dana sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, wanda jiya Alhamis shima yace Moscow na jefa kanta cikin wata matsala mai tsada, saboda ta ki ta dakatar da ‘yan aware.
XS
SM
MD
LG