Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Nayi Wa Musulmi Fatan Alheri


Mutane suna kallon yadda wata ya keta gaban rana yayin husufin rana a Najeriya ranar uku ga watan Nuwamban shekarar 2013.

Musulmi a fadin duniya suna shirye-shiryen fara azumin watan Ramadana don azumtar watan da kuma yin ibadoji a cikinsa, a yayin da wasu kasashen ma sun tashi da azumin.

Tuni Shugaban Amurka a jiya Laraba ya mika sakon fatan alherinsa ma’azumtan dake Amurka da ma duniya baki daya.

Kasashen Saudiyya, Misara, Iran da Indonesia sun bayyana sanarwar ganin watan da ya fara a yau Alhamis. Wata ne dai da Musulmai ke kamewa daga ci da sha tare da yawaita ibada.

Shugaba Obama na sa ran gayyatar Musulman Amurka zuwa fadar White House don yin buda baki da niyya girmamawa ga watan na Ramadan da kuma yabawa gudunmawar Musulman na Amurka a fadin kasar.

XS
SM
MD
LG