Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Ya Jinjina Ma Marigayi Dan Mataimakinsa


Jana'izar Beau Biden

Shugaban Amurka Barack Obama da sauran manya sun jinjina ma marigayi dan Mataimakin Shugaban Amurka Beau Biden.

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi jinjina mai sosa rai a wurin jana'izar dan Mataimakin Shugaban Kasa Joe Biden, mai suna Beau Biden, inda ya bayyana mamacin da "mutum mai matukar nuna kauna, wanda kuma aka saka masa da matukar kauna."

Mr. Obama na daya daga cikin mutyane da dama da su ka jinjina ma Beau Biden a jiya Asabar, a Majami'ar Katolika ta St. Anthony of Padua da ke Wilmington na jihar Delaware.

Beau Biden, tsohon Attoni-Janar na jihar ta Delaware, ya mutu ne sanadiyyar kansar kwakwalwa mako guda da ya gabata, ya na mai shekaru 46 da hauhuwa.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG