Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Ya Kaddamar Cibiyar Tarihin Bakar Fatan Amurka


Sabon cibiyar tarihin bakar fatar Amurka.
Sabon cibiyar tarihin bakar fatar Amurka.

Yau Asabar a hukumance aka bude cibiyar ga al'uma.

Da yake magana a bikin kaddamar da cibiyar tarihi da aladu na bakar fatar Amurka, shugaban Amurkan Barack Obama yace tarihinsu jigo ne ko yana da tasiri ga tarihin Amurka wanda yake cike da tarihin magabatan kasar.

"Galibi muna biris ko muna manta labaran mliyoyin Amurkawa, wadanda suma hakika suna cikin tarihin gina kasan nan," Inji Mr. Obama.

Bayan shekaru ana aikin gina wannan cibiyar tarihin, wannan sabuwar cibiyar tarihi na bakar fatan Amurka a tsakan-kanin irinta na wasu tarihan da ala'du, yau Asabar ne a hukumance aka bude shi.

Mr. Obama yace cibiyar tarihin, zata bada labarin Amurka da zai taimakawa wajen karfafa sulhu na waraka a zukatun al'uma.

Cikin wadand suka halarci bikin na yau harda tsohon shugaban Amurka George Bush karami, wand a ya sanya hanu kan dokar da ta bada izirnin a fara aikin ginin cibiyar tarihin,da kuma dan majalisar wakilan Amurka mai wakiltar jahar Georgia, John Lewis, wanda har wayau, gwarzo ne a fagen yaki da karev'yancin tsiraru, John Lewis. Mr Obama ya kira cibiyar da cewa, ta dara a zaman gini kawai, yace wannan mafarki ne da ya tabbata."

Domin kaddamar da bude cibiyar tarihin a hukumance, shugaba Obama da uwargidansa Michelle, sun kada wata karrawa mai ciuke da tarihi daga wata majami'ar bakar fata dake nan Amurka.

Jiya jumma'a shugaban na Amurka ya gayawa taron mutane 750 a wani bangare na fadar White House, wadanda suka hallara domin bikin bude wannan cibiya yazo tamkar sara kan gaba, furicin da ya baiwa mahalarta wadanda galibinsu bakar fatar Amurka ne dariya haer suka tafa, saboda nasabar haka da shugabancinsa wanda yake zuwa karshe, da kuma abubuawa da suke faruwa a Charlotte da kuma Oklahoma. Inda ake fama da zanga zanga kan kashe bakaken fata da jami'an Sanda suka yi.

XS
SM
MD
LG