Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Oabama Yana Goyon Bayan Britaniya Ta Ci Gaba Da Zama A KungiyarTarayyar Turai.


Shugaban Amurka Barack Obama da PM INgila David Cameron, a wani taro da manema labarai a London ranar jumma'a.

Amma wasu 'yan kasar, suna zargin shugaba Obama da yin shishshigi cikin harkokin cikin gida na kasar.

Shugaban Amurka Barack Obama, ya tsoma baki cikin zazzafar muhawara da ake yi a Britaniya kan kuri'ar raba gardamar da 'yan kasar zasu ranar 23 ga watan Yuni, kan ko kasar zata ci gaba da zama cikin kungiyar tarayyar turai.

"Bana jin kungiyar tarayyar Turai tana rage tasirin Britaniya a duniya, sai dai ma ace tana kara bunkasa shi," inji shugaban na Amurka, a wani taro da manema labarai na hadin guiwa, da PM Ingilan, David Cameroon, bayan da suka gana jiya jumma'a.

Kalaman na Mr. Obama, ya karawa shugaban na Britaniya kwarin guiwa, kan matsayarsa na goyon bayan kasar ta ci gaba da zama cikin kungiyar tarayyar turai.

Amma kalaman na shugaba Obama sun harzuka masu adawa da wannan shiri a Ingila, wadanda suke ganin maganar da shugaban na Amurka yayi, shishshigi ne, cikin harkokin cikin gida na kasar.

A cikin wata makala da aka wallafa a jaridar "The Telegraph," da saukar jirgin saman shugaban na Amurka a daren Alhamis, a wata tashar jirgin sama dake bayan garin London, shugaban na Amurka, yayi kira ga Britaniya ta ci gaba da zama wakiliya a kungiyar tarayyar turai.

Dangantaka tsakanin Amurka da Britaniya, shine mu'amala da shugabannin a Washington suke da ita, da kasar Ingilan tun zamanin mulkin Winston Churchil, wacce ake dauka a zaman "ta musamman ce," kuma Amurka tana kallon ci gaba da kasancewar kasar cikin kungiyar, tamkar wakilci ne ga Amurka a kungiyar hada kan kasashen turan, mai wakilai 28.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG