Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Zai Fara Ziyarar Aiki A Jamus


Angela Markel Shugabar Gwamnatin Jamus da Shugaban Amurka Obama a Taron G7, Munich, Yuni 8, 2015.
Angela Markel Shugabar Gwamnatin Jamus da Shugaban Amurka Obama a Taron G7, Munich, Yuni 8, 2015.

Shugabbanin biyu zasu tattauna kan batutuwa da suka hada da cinikayya, da tsaro da sauransu.

Shugaban Amurka Barack Obama, tareda shugabar Jamus Angela Merkel, zasu tattauna kan batutuwa da suka shafi tattalin arzikin duniya, da ta'addanci, da tsaro, da ma wasu lamura na daban, lokacinda shugaban na Amurka ya kai ziyarar aiki a Jamus.

Lahadi ake sa ran shugaba Obama, zai gana da shugaba Merkel, jim kadan bayan ya isa birnin Hanover.

Bayan sun gana da manem alabarai, shugabannin biyu, zasu yi bikin bude babbar kasuwar baje koli, da aka tallata zaman mafi girma irinsa kan harkokin fasaha, a fadin duniya. Masu shirya baje kolin, suna sa ran mutane 'yan kasuwa a fannin fasaha su 6,500 ne zasu baje kolinsu, kuma jama'a fiyeda dubu metan ne daga ksashen duniya 70, zasu halarci kasuwar baje kolin.

Jami'an fadar White House sun ce bikin baje kolin, ya nuna irin muhimmancin hada kai tsakanin Amurka da Jamus a fanoni daban daban, ciki harda cinikayya da kasuwanci.

Hakan nan shugabannin biyu suna fatar zasu kara nema da kuma bada goyon baya ga yarjejeniyar cnikayya da aka fi sani da TTIP a takaice. Amurka da tarayyar Turai ne suke shawarwari kan kulla wannan yarjejeniya.

Shugaban Amurka yana ganin da muhimmancin gaske ya ziyarci jamus a shekararsa ta karshe na shugabancin Amurka, domin shugaba Merkel, ta kasance abokiyar aikinsa ta kud da kud, a duk tsawon shugabancinsa," inji mukaddashin mai baiwa shugaban shawara kan gharkokin tsaro.

XS
SM
MD
LG