Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Karrama Ba'amurikiyar Da Ta Koyas A Kauyukan Jamhuriyar Niger.


Reilly Knop, Ba'amarikiyar da ta yi koyaswa a kauyukan Niger
Reilly Knop, Ba'amarikiyar da ta yi koyaswa a kauyukan Niger

Ofishin jakadancin Amurka a Jamhuriyar Niger ya shirya wata kwarya-kwarayar buki domin karrama wata matashiya ba’amurkiyar da ta bada kyakyawan misali a tsawon watanni 10 da ta shafe tana koyarda turancin ingishi a wasu makarantun birnin Yamai da da wasu kauyuka.

Reilly Knop, wata malamar da gwamantin Amurka ta aika Jamuhuriyar Niger domin yiwa kasarta hidima, ta shafe watanni 10 tana karantarda turancin ingilishi a makarantun ESCAE da IFTIC da koyas da matasa ilimin sana'o'i a kauyuka.

Reilly ta bayyana yadda take jin alamun za ta yi kewar dalibanta da ma sauran abokan aikinta, saboda a cewarta tayi zaman mutunci da su a tsawon lokaci da ta yi ta na aiki dasu.

Reilly da Jakadan Amurka Eric Whitaker a Niger
Reilly da Jakadan Amurka Eric Whitaker a Niger

Lura da yadda wannan matashiya ta gwada kwarewa akan aiki da kuma yadda ta zauna lafiya da jama’ar dake tare da ita, ya sa ofishin jakdancin Amurka a Yamai, shirya wata kwarya-kwaryar buki, domin bata damar yiwa abokan zamanta bankwana a hukumance inji Alhaji Idi Barau jami’in hulda da manema labarai na ofishin jakadancin Amurka a Niger.

A cewar Abba Kyari, wani malami dake koyarwa a makarantar IFTIC sun koyi abubuwa da dama daga Reilly Knop, a tsawon watanni 10 na aikin hidimar da ta yiwa Niger da sunan gwamnatin Amurka.

Shekaru sama da 30 kenan da cibiyar raya al’adun Amurka ke karantar da turancin ingilishi a Niger, abinda ya baiwa dubban jama’a, galibinsu matasa, damar lakantar karatu da rubutun wannan harshe da a yau suke amfana da shi a harkokinsu na yau da kullum. Saboda haka jakadan Amurka a Niger Ambassador Eric P. Whitaker, ya kara jaddada ci gaban wannan shiri na horasda jama’a.

A saurari rahoton Souley Barma domin karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG