Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ofishin Jakadancin Amurka A Nijar Ya Shirya Liyafar Bukin 'Yancin Kai


Bukin 'yancin kan Amurka a Nijar
Bukin 'yancin kan Amurka a Nijar

Yayinda Amurkawa ke bukin tunawa da ranar samun ‘yancin kan kasar, ofishin jakadancin Amurka a Nijar ya shirya liyafar cin abinci domin karrama wannan rana ta 4 ga watan yuli.

Da yake jawabi a yayin wannan buki d ya sami halartar jami'an gwamnatin Nijer jakade Eric Whitaker ya yabawa abinda ya kira kyakkyawar huldar dake tsakanin Nijer da Amurka, kasashen da yace suna da alkibla guda wajen aiyukan bunkasa demokaradiya, da ayyukan samarda tsaro, da habbaka tattalin arziki.

A watan Janairu ta wannan shekarar, 2018, gwamnatocin biyu suka kaddamar da wadansu manyan ayyukan inganta rayuwar jama’ar Nijer musamman a yankunan karkaka, ta hanyar wani shirin da ake kira MCCompact da aka warewa milyan 437 na dallar Amurka, banda miliyan 18 da Amurka ta talllafawa Nijer domin yaki da masassarar cizon sauro..

Matasa

Jamhuriyar Nijer na daga cikin kasashen dake kan gaban wadanda Amurka ke taimakawa matasa kamar yadda wadansu bayanai ke nuna cewa, matasan wannan kasa sama da 500 ne suka mori wani tsarin samarda madogara baya ga dimbin wadanda suka samu horo albarkacin shirin nan na YALI dake karfafawa matasan Afirka guiwa domin ciyarda al’umar wannan nafiya sama.

Ta'addanci

Jakaden Amurka a Nijar ya bayyana cewa,yaki da ta’addanci domin samarda tsaro a Nijer da sauran kasashe makwafta na daya daga cikin muhimman abubuwan da suke ciwa Amurka da kuma Jamhuriyar Nijar tuwa a kwarya a halin yanzu. Jakaden Eric Whitaker yace, gwamantocin kasashen biyu na da cikaken hadin kan da zai basu damar nasarar cimma wannan guri. Ya kuma jajantawa dukan jama’ar da suka rasa ‘yan uwansu a dalilin yaki da ta’addanci.

Ya kuma jadada cewa, Amurka za ta ci gaba da taimakawa wannan kasa a dukkan fannonin da ta saba yi dommin kyautata rayuwar jama’a…

Saurari rahoton da wakilinmu a birnin Yamai Souley Moumouni Barma ya aiko mana.

Bukin Samun 'yancin kan Amurka-2:40"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG