Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddamar Soke Bizar 'Yan Najeriya A Saudiyya


HAJJ
HAJJ

Fasinjoji 87 hukumomin Saudiyyan suka amince suka shiga kasar cikin mutum 264 inda suka sa aka mayar da 177 Najeriya.

ABUJA, NIGERIA - Jirgin ya taso ne daga filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke legas, ya bi ta filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano a daren Lahadin da ta gabata.

Kuma ya isa babban birnin Saudiyya a ranar Litinin ba tare da wata matsala ba. Amma da saukarsu, sai mahukuntan Saudiyyar suka sanar da soke bizar izinin shiga kasar.

Sai dai daga cikin fasinjoji 264 da suka taso a cikin jirgin zuwa kasar Saudiyya , 87 ne kawai hukumomin Saudiyya suka wanke su, bayan da jami'an ofishin jakadancin Najeriya suka shiga tsakani.

A lokacin da yake amsa tambayar ko mene ne ka iya zama musabbabin soke biza mai yawa irin wannan, daya cikin masu kamfanin jigila a Najeriya Alhaji Farouk Koki ya ce bizar kala biyu ce.

Wadanda suke cikin wannan jirgin, akwai masu bizar Umrah da kuma bizar da ake ce mata 'E' biza wacce ta ke kaman ta kasuwanci ce, amma ba wadda aka sani wadda ake ce mata ' ENTRY' biza ba, domin hukumomin Saudiyya sun kirkiro wannan biza ne saboda a samu saukin kasuwanci.

Ya kara da cewa,'yan Najeriya sai suka rungumin wannan bizar, suke ta ba mutane wadanda ke zuwa su zauna a Saudiyya, saboda haka hukumomi suka ga kaman wani abu daban ne ya kawo su ba kasuwanci ba.

Hakan ya sa suka tantance masu biza ta Umrah su 87, sai suka bar wadanda ke da biza ta daban su 177 aka dawo da su gida.

A lokacin da ya ke tofa albarkacin bakinsa a game da wannan mataki da kasar Saudiyya ta dauka, shi ma kwararre a fannin jigilar fasinjoji Alhaji Najib Mohammed Tukur ya ce ba wai don mutum yana da biza mai kyau ne yake nuna cewa dole idan ka zo wannan kasa, dole ne sai ka shiga wannan kasa ba, domin tsarin yadda ya ke.

Amma jami'i a ofishin jakadancin Najeriya da ke Saudi Arabia Ambasada Husseini Bello Kazaure, ya ce suna daukan wani mataki domin gano matsalar, kuma daga dukkan alamu sun gano bakin zaren, kuma suna ta bincike da tattaunawa tsakanin gwamnatin Saudi Arabia da kuma gwamnatin Najeriya.

Kazaure ya kara da cewa, wannan ba wani abu ne da zai ta da jijiyan wuya ba ne.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:

Takaddamar Soke Bizar 'Yan Najeriya A Saudiyya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG