Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Olukoyede Ya Sha Alwashin Yin Murabus Matukar Ba'a Gurfanar Da Yahaya Bello Ba


Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) Ola Olukoyede
Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) Ola Olukoyede

A hirarsa da manema labarai a shelkwatar Hukumar EFCC dake shiyar Jabi ta birnin Abuja a yau Talata, shugabanta ya sha alwashin sauka daga kan kujerarsa matukar ba'a gurfanar da Yahaya Bello ba.

WASHINGTON DC - Shugaban Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin ta'annati, Ola Olukoyede ya sha alwashin bin diddigin batun gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello har izuwa karshe.

Ya kuma sake shan alwashin hukunta dukkanin wadanda suka yi tarnaki wajen hana kama tsohon gwamnan.

Hukumar EFCC na kokarin gurfanar da Yahaya Bello ne a bisa tuhume-tuhume 19 dake da nasaba da zargin halasta kudaden haram da cin amana da wawure kudaden da yawansu ya kai naira biliyan 80 da miliyan 200 da doriya.

Ya cigaba da cewar koma me wani zai yi kuma komai yawan sukar da za'a yiwa hukumar, shi da jami'ansa ba zasu saurara ba wajen tsaftace kasar nan.

Olukoyede yace EFCC na bukatar samun goyon bayan 'yan Najeriya domin samun nasara inda ya jaddada cewar rashin nasarar hukumar ta Najeriya ce baki daya. Ya kara da cewar kokarin da ake yi a halin yanzu ya taimaka wajen farfado da darajar naira da kasuwar musayar kudade.

A wani labarin mai nasaba da wannan kuma, Hukumar EFCC ta mika kwafin takardar tuhumar zargin zambar naira bilyan 80 da ake yiwa tsohon gwamnan ga lauyansa, Abdulwahab Muhammad.

Hakan ya biyo bayan umarnin da mai shari'a Emeka Nwite na Babbar Kotun Abuja ya bayar sakamakon kin bayyanar Yahaya Bello a gaban kotun.

Alkalin yayi dogaro da sashe na 384 karamin sashe na 4 na dokar hukunta manyan laifuffuka ta 2015, inda ya umarci lauyan tsohon gwamnan ya karbi kwafin takardar tuhumar a madadinsa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG