Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Olympics: Dan Tseren Maza Na Mita 100 Mai Wakiltan Ghana Bai Kai Labari Ba


Benjamin Azamati-Kwaku

Dan wasan tseren Ghana mafi sauri, Benjamin Azamati-Kwaku ya roki ‘yan kasarsa gafara a kan gazawarsa na kai ga tseren maza na mita 100 a wasan karshe a wasannin Olympic shekarar 2020.

Rawar gani da Azamati-Kwaku ya taka a ranar 26 ga watan Maris shekarar 2021, inda ya kashe tarihin kasa da Leo Myles-Milles ya kafa a (1988) na kamala tseren cikin dakiku 9.98, yayin da shi Azamati ya yi tseren cikin dakiku 9.97, lamarin da ya baiwa ‘yan Ghana da dama kwarin gwiwar ya kimtsa ya fafata da shahararrun ‘yan wasan duniya.

Amma tseren mita 100 da ya fara yi a Olympic a ranar Asabar shine ya zo na hudu da dakiku 10.13 a bayan wani dan wasan Australia Rohan Browning na farko da Yhan Blake na biyu da kuma dan wasan Birtabiya Chijindu Ujah

Da ya gano kuskurensa, mi gudun tseren dan shekaru 23 ya yi amfani da shafinsa na sada zumunta ya mika rokon gafararsa ga kasar Ghana baki daya.

“A yi hakuri! Gaskiya na gaza kai labari,” abin da ya rubuta a kan shafinsa kenan.

Ya ce “abubuwa zasi inganta nan gaba. Yanzu da na gano kura kurai n azan faro gyara daga wurin. Ina matukar murna da goyon baya da kuka bani. Na ji irin kaunar da kuka nuna min. Zan yi alfahari da haka kana zan yi aiki tukuru a wasannin gaba,” inji shi.

Benjamin Azamati-Kwaku zai karu da Joseph Paul Amoah da Sean Sarfo Anti da kuma Joseph Oduro Manu a wasan tsaren maza na zari-ka-ruga na mita 100 sau hudu.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG