Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ondo Ta Samu Mutum Na Farko Da Ya Kamu Da COVID-19


Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu
Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu

Jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya ta bayyana samun mutum na farko da ya kamu da cutar coronavirus.

Gwamna Oluwarotimi Akeredolu ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a.

“A yammacin yau mun samu bayanai kan mutum na farko da ke dauke da cutar #COVID-19 a jihar Ondo. Tuni an killace shi za kuma a ba shi kulawa.” Ekeredolu ya ce.

Jaridar Daily Trust wacce ita ma ta ruwaito labarin ta ce mutumin da aka samu dauke da cutar soja ne da ya dawo daga India, ko da yake hukumomin jihar ba su tabbatar da hakan ba.

A halin da ake ciki gwamna Ekeredolu ya ce ana kokarin gano mutanen da mutumin ya yi mu’amulla da su domin a killace su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG