Wannan ne kofin babbar gasar Tennis na 3 da matashiyar ‘yar shekaru 22 ta lashe, bayan da tayi nasarar lashe gasannin US Open a shekara ta 2018 da kuma Australian Open ta shekarar 2019.
Osaka ‘yar kasar Japan da ke matsayin mace ta 4 a duniyar Tennis, ta doke Azarenka ne da turmi biyu da daya; 1-6, 6-3, 6-3, a wasan na karshe da suka kwashe tsawon sa’a daya da mintuna 53 suna fafatawa, a filin wasa na Arthur Ashe da ke New York, wanda yake wayam ba ‘yan kallo.
Azarenka ‘yar kasar Belarus mai shekaru 31, ita ce ta ja gaba a farkon soma wasan, inda a cikin mintuna 26 ta yi wa Osaka turmi daya, to amma daga bisani Osaka din ta yunkuro ta yi waiwayen baya, ta kuma yi nasara a turmi na biyu da na uku.
Osaka ta yi kwance rigingine tana kallon sama a cikin filin wasan cikin murna, jim kadan bayan da tayi nasarar lashe wasan.
‘Yar wasar ta yi amfani da takunkumin rufe fuska a lokuta da dama a yayin da ta ke shiga filin wasa, masu dauke saunayen mutane bakar fata daban-daban da ‘yan sanda farar fata suka kashe, domin karrama su, da kuma nuna goyon baya kan fafutukar yaki da wariyar launin fata.
Facebook Forum