Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Osimhen Ya Yi wa Kungiyarsa Ta Napoli Yaji


Osimhen
Osimhen

Kwantiragin Osimhen zai kare a shekarar 2025, amma akwai rahotanni da ke nuna cewa mai yiwuwa ya bar Napoli a watan Janairu.

Dan wasan gaba na kungiyar Napoli a kasar Italiya, Victor Osimhen, ya goge dukkan hotunansa da yake sanye da rigar kungiyar a kafafen sada zumuntarsa.

Osimhen wanda dan asalin Najeriya ne, ya dauki wannan mataki saboda kungiyar ta Napoli ta wallafa wani bidiyo a kafar sada zumunta inda take tsokanar dan wasan kan fenaritin da ya zubar.

Dan wasan gaban ya zubar da fenaritin a wasansu da Bologna na ranar Lahadi inda aka tashi da ci 0-0.

A ranar Talata kungiyar ta wallafa bidiyon Osimhen a kafar TikTok wanda ke nuni da alama ta nuna rashin iyawa, lamarin da ya fusata dan wasan.

Tuni Napoli ta cire bidiyon a kafar sada zumunta.

A martanin da ya mayar, Osimhen ya shiga shafukansa na sada zumunta ya goge kusan dukkan hotunansa da yake sanye da rigar kungiyar.

Agent din Osimhen ma ya nuna fushinsa kan bidiyon da kungiyar ta wallafa.

Kwantiragin dan wasan da kungiyar zai kare a shekarar 2025, amma akwai rahotanni da ke nuna cewa mai yiwuwa ya bar Napoli a watan Janairu.

Osimhen ne dan wasan da ya fi zura kwallaye a kakar wasa ta bara da kwallaye 26.

Ya zuwa yanzu yana da kwallaye uku a wasanni biyar a wannan kakar wasa.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG