Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan: Bamabamai Biyu Sun Fashe a Peshawar


Tashin Bam a Pakistan

Wasu bama bamai guda biyu sun fashe a wurare daban daban awa daya tsakani, wadanda suyi sanadiyyar raunata jami’an tsaro uku a Birnin Peshawar dake kasar Pakistan a safiyar yau Litinin..

Bam na farko ya fashe ne a bakin kofar shiga makarantar mata amma bai jiwa kowa ciwo ba. Jami’an Yansandan yankin sun ce akwai bama bamai biyu a wurin da abin ya faru amma daya bai tashiba. Jami’an dake aikin cire bama bamai sunyi kokarin lalata Bam din guda da bai tashi ba.

Bam na biyu da ya tashi kuwa a wani yankin ne daban, wanda ya wata motar jami’an yaki da aiyyukan ta’addanci wacce ke kan hanyar dawowa daga harin da aka kai a makarantar farko. An kai jami’an da suka raunata asibitin da ke kusa mai suna Asibitin Lady Reading.

Har izuwa yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG