Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Da China Sun Karyata Batun Wata Yarjejeniyar Sirri


China Da Pakistan

Pakistan da China sun karyata tare da bayyana wasu rahotannin kafafen yada labarai a matsayin "shirme da kage," rahotannin dai sun ce kasashen kawayen kud-da-kud suna gudanar da wani binciken hadin gwiwa a sirrance domin kera makamai daga kwayoyin cututtuka, abinda ya saba wa yarjejeniyar kasa da kasa.

Wata kafar yada labarai a Australia, ta The Klaxon, a wani rahoton binciken kwakwaf da ta fidda a makon da ya gabata, ta yi zargin cewa Beijing da Islamabad sun kulla wata yarjejeniyar sirri ta shekaru uku don fadada kwarewarsu ta hada makaman kwayoyin cututtuka, ciki har da gudanar da bincike kan shirye-shirye da yawa masu alaka da kwayar cutar Anthrax mai kisa.

Rahoton ya ambato wasu majiyoyin bayanan sirri da yawa suna cewa cibiyar nazarin kwayoyin cututtuka ta Wuhan a China, ta bada rancen kudi da taimako ta fannni kimiyya don a kafa cibiyar ta sirri a Pakistan. Cibiyar nazarin ta Wuhan ta na ba kwararru a fannin kimiyya na Pakistan horo akan yadda za su sarrafa kwayoyin cuta da kuma tattara bayanai da nazarin kwayoyin cuta masu sarkakiya, domin taimaka wa Pakistan ta kirkiri kundin bayanan kwayoyin cuttuttuka na kanta.

Wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ta karyata zancen, ta hakikance kan cewa babu wani abun sirri game da gina cibiyar da rahoton ya bayyana, sanarwar ta kuma ce ana amfani da cibiyar ne don nazari da binciken abubuwa da ke barazana ga lafiya masu bullowa, da kuma sa ido da gudanar da bincike kan barkewar cututtuka.

Facebook Forum

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG