Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan ta hana mai kamfanin jirgin da ya fado barin kasar


Baraguzan jirgin Saman da ya fadi a Pakistan.

Kasar Pakistan ta hana mai kanfanin jirgin saman da wani jirginsa ya fadi ya hallaka mutane 127, barin kasar.

Kasar Pakistan ta hana mai kanfanin jirgin saman da wani jirginsa ya fadi ya hallaka mutane 127, barin kasar.

Ministan cikin gidan Pakistan Rehman Malik y ace an hana Farooq Bhoja fita daga Pakistan a yayin da jami’an harkokin sifiri ke binciken hatsarin na jiya Jumma’a da ya hallaka dukkannin mutanen da ke cikin jirgin.

Shaidu sun ce jirgin samfurin Boeing 737 ya rikito ne yayin da ake wani hadari da tsawa a kusa da filin jirgin saman kasa da kasa na kasar, kuma da alamar ya kama da wuta tun ma kafin ya radu da kasa. Wani jami’in sifiri dai ya ce mummunan yanayi ne sanadin hatsarin, to amman ba a tabbatar da musabbabin ba tukunna. An gano na’urar tattara bayanan tafiyar jirgin, wanda ke da muhimmanci sosai ga binciken.

Tun da asubahin yau Asabar aka ga sojoji da masu taimakon gaggawa na nemo gawarwaki cikin baraguzan jirgin.

Kamfanin Jirgin Saman na Bhoja Air ya taba tsaida aiki na tsawon sama da shekaru 10, to amman sai ya dawo da aiki cikin watan Maris da wasu gwanjunan jirage da - wanda jami’an sirifirin jirgin sama su ka ce hakan ba bakon abu ba ne.

A sa’ilinda kamfanin jirgin ya sha zirga-zirga tsakanin Lahore da Karachi, tafiyar ta jiya Jumma’a da ta gamu da hatsari it ace karo na farko da kamfanin jirgin ya doshi birnin Islamabad. Jami’ai dai sun ce jirgin, wanda hayansa kamfanin Bhoja ya yi, ya yi ta aiki na tsawon shekaru 30.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG