Kasar Pakistan ta ce dakarunta sun harbo wasu jiragen yakin Indiya guda biyu, da suka ratsa ta kan iyakar yankin nan da kasashen biyu suka dade suna rigima a kansa, watau yankin Kashmir.
Wani kwamandan sojan Pakistan Manjo-janar Asif Ghafoor, ya ce an kama daya daga cikin direbobi jirgin na India bayan da jirgin ya fadi, kuma yanzu haka yana tsare a sansanin Kashmir bangaren rikon Pakistan, yayin da daya jirgin kuma ya fadi a bangaren rikon India na Kashmir din.
Ya zuwa yanzu, babu wani bayani daga hukumomin kasar Indiya game da zargin da kasar ta Pakistan keyi, koda yake kafofin watsa labaru na Indiya, sun ce an samu dukkan direbobin jiragen yakin na India, kuma an san inda suke.
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 21, 2023
Saudiyya Ta Ce Ranar Alhamis Watan Azumi Zai Kama
-
Maris 17, 2023
Kotun ICC Ta Ba Da Izinin Kama Putin
-
Maris 13, 2023
Shugaba Buhari Ya Taya Xi Jinping Murnar Sake Lashe Zabe
Facebook Forum