Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Ta Kara Damarar Yaki da Ta'addanci


Shugaban Gwamnatin Pakistan Shahid Khaqan Abbasi
Shugaban Gwamnatin Pakistan Shahid Khaqan Abbasi

Gwamnatin Pakistan da ta Amurka sun tattauna akan hanyoyin da zasu bi wajen samar da zaman lafiya a Afghanistan.

Shugaban gwamnatin Pakistan, Shahid Khaqan Abbasi, yace a shirye suke wajen yakar ta'addanci. Ya bayyana hakan ne a yau litinin a wata tattaunawa da yayi da sakataren tsaron Amurka Jim Mattis .

Ya kara da cewa " babu wanda yakeson zaman lafiya a Afghanistan sama da Pakistan." Ya kuma jaddada cewa Amurka da Pakistan sunada kuduririka iri daya.

Zaman tattaunawar da sukayi a yau din a birnin Islamabad ya samu halartar ministan harkokin cikin gidan Pakistan, mai ba da shawara akan harkokin tsaron kasa da kuma shugaban binciken sirri.

Sai dai Mattis bai yi wani sharhi ba a bainar jama'a kan taron ranar litinin din. Gabannin ziyarar da ya ksi Islamabad yace bashi da niyyar matsawa Pakistan illa dai yana bukatar su cika alkawarin da suka dauka na yaki da ta'addanci.

"Inada yakinin cewa zamu iya aiki tukuru wajen cimma matsaya sannan muyi aiki tare", a cewar Mattis.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG