Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Ta Sanar Da Gwada Makami Mai Linzami


Makamin da Pakistan ta gwada da ta lakabawa suna Babur

Makami mai linzami da Pakistan ta gwada a karkashi teku ta ce ta yi ne domin ya zama wa India kashedi, kada ta nemeta da yaki kamar yadda suka saba yi can baya

Pakistan ta sanar jiya Alhamis cewa, ta yi nasarar gwada makami mai linzami da za'a iya goyawa makaman nukiliya. An harbo makamin daga jirgin ruwan yaki mai tafiya karkashin kasa, kuma zai iya tafiyar kilomita 450.


Wannan makamin mai linzami da Pakistan ta kera mai suna Babur, an harba shi ne a karkashin ruwa kuma ya isa daidai inda ake bukatar ya isa, acewar wata sanarwar sojin kasar.


Wannan makami mai linzami za'a iya goya masa makamai iri daban daban ,kuma ya baiwa Pakistan wani zabi na kai farmaki.


Pakistan ta ce tana shirinta na kera makaman nukiliya da masu linzami ne, domin India, kuma hakan acewarta ya hana babbar makwabciyarta mai karfin soji kawo mata yaki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG