Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malala Matashiyar Da Ta Samu Lambar Yabo Ta Isa Pakistan Yau


Malala Yusufzai
Malala Yusufzai

Malala 'yar Pakistan, matashiyar da 'yan Taliban suka harba akai saboda tanayakuwar sa yara mata makaranta ta ziyarci kasarta a karon farko tun daga lokacin da aka fitar da ita shekaru shida da suka gabata

Yau Alhamis ne ake sa ran matashiyar nan data samu lambar yabo ta Nobel, Malala Yusufzai ‘yar kasar Pakistyan, ta koma kasar a karon farko tun bayan da wani dan kungiyar Taliban ya harbe ta akai shekaru shidda da suka wuce saboda kawai tana yekuwar asa yara mata makaranta.

Wannan yarinyar dai tayi suna a kasashen duniya,domin kokarin ta na fafitika, amma a Pakistan ra’ayoyi sun banbanta a cikin kasar gameda da ita, a bangaren masu ra'ayin mazan jiya suna mata kallon yar farautar kasahen yammacin turai mai niyyar kunyata kasar ta.

A cikin ziyarar ta na kwanaki hudu ana sa ran Malala zata gana da Prime Ministan kasar Shahid Khaqan Abbasi, sai dai sauran abubuwan da za ta yi ba a bayyana su badomin dalilai na tsaro inji wani jamiin gwamnatin kasar.

Malala ‘yar shekaru 20 da haifuwa, tana tare da iyayen ta ne wadanda sune ke mata rakiya, ta sauka filin jirgin saman kasa da kasa na Islamabad da aka lakabawa sunan tsohuwar PM kasar mai rasuwa Benezir Bhotto, kuma an tsaurara matakan tsaro lokacin data sauka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG