Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Ta Nada Mutumin Da Zai Gaji Nawaz Sharif


Shahid Khaqan Abbasi, PM Pakitsan na wucin gadi.
Shahid Khaqan Abbasi, PM Pakitsan na wucin gadi.

Wadanda aka nadan shine Shahid khaqan Abbasi, wanda kamin nadin shine ministan man fetur na kasar.

A Pakistan, Jam'iyyar da take mulkin kasar PMLN a takaice, ta zabi mutumin da zai zama PM kasar na wucin gadi,mataki da ya janyo suka daga 'yan hamayya, kwana daya bayan da kotun kolin kasar ta kori PM Nawaz Sharif, saboda kariya kan kadaror da ya boye a ketare.

Sharif dan shekaru 67 da haifuwa, ya jagoranci taron gaggawa na jam'iyyar a birnin Islamabad, inda shugabanni suka zabi Ministan mai Shahid khaqan Abbasi, ya gaji PM Sharif, na tsawon kwanaki 45.

Duk da nadinsa, Mr Abbasi ba zai kama aiki ba sai bayan da majalisar dokokin kasar ta kada kuriar amincewa da nadinsa.

Shugaban kasar Mamnoon Hussain,ya bukaci majalisa tayi taro ko zama na musamman ranar Talata, a majalisar wakilai, ind a jam'iyyar Nawaz Sharif take da rinjaye.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG