Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Pakistan,'Yan Kunar Bakin Wake Biyu Sun Halaka Mutane Hamsin, Suka Raunata Wasu 100, a Yankin Kabilu.


Hoton wasu da harin kunar bakin wake ya rutsa da su a yankin kabilu na Pakistan a yau litinin.

Maharan sun yi shigar 'Yansanda kan babura a suka tarwatsa kawunansu a wani gidan gwamnati da ake taro da shugabannin al'uma da na gwamnati kan hanyoyin yakar mayakan sakai a yankin.

Litinin din nan hukumomin Pakistan sun bada labarin ‘yan kunar bakin wake biyu sun tarwatsa kawunansu a wani taron kafa rundunar masu adawa da kungiyar Taliban. An shirya taron ne a yankin arewa maso yammaci na kabilu,suka halaka mutane hamsin,suka kuma raunata wasu 100.

Hukumomin sun ce maharan sun yi shigar ‘yansanda kan Babura,yayinda suka tada nakiyoyi cikin gundumar Mohmand, kusa da kan iyakar kasar da Afghanistan. Wani babban jami’in gwamnati dake yankin,Amjad Ali Khan, yace an kai harin ne a wani taron dattijai da jami’an gwamnati suke taro a wani babban ginin gwamnati a Ghalanai.

Cikin wadanda aka kashe har da iyayen jama’a,’Yansanda,ma’aikatan kananan hukumomi,d a’yan Jarida biyu. Babu wanda ya fito nan da nan ya dauki alhakin kai wan nan hari.

Rundunar sojojin Pakistan ta juma tana fafatawa dad a mayakan sakai a Mohmand,amma ta kasa murkushe kungiyoyin Taliban da masu alaka da al-Qaida. Mayakan sakai suna auna hare hare kan kabilu dake yankin,wadanda sojojin kasar suke karfafawa guiwar suka kafa kungiyoyin mayakan sakai domin adawa da sauran kunigoyoyi dake yakar gwamnati.

Duka dai a yau litinin,a yankin Wziristan,jami’an Pakistan sun bada labarin jirgin yakin Amurkan nan da bashi da matuki ya kai farmaki, ya kashe mutane biyar, da ake jin mayakan sakai ne. sun ce an auna harin kan wani gida da wata mota a kauyen khushali.

XS
SM
MD
LG