Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansanda A Sweden Sun ce Fashe fashe Biyu A Babban birnin Kasar Stockholm, har Suka Kashe Mutum Daya,Da Jikkata Wasu Biyu,Ta'addanci Ne.


Wan nan hoto,'yan kwana-kwana ne a birnin Stockholm suke kashe wutar da ta kama wata mota wacce ake jin daga cikin motar ce aka ji wata fashewa jiya Asaabar.

Kakakin rundunar "yansandan kasar Anders Thornberg,ya gayawa taron manema labarai cewa binciken da ake gudanawar ahalin yanzu ya dogara ne kan dokokin ta'addanci da kasar ta tanada,duk da haka ba a zafafa matakaan tsaro ba.

‘Yansanda a Sweden sunce fashe fashe biyu da suka auku a tsakiyar birnin Stockholm, har mutum daya ya mutu wasu biyu suka jikkata,yunkurin ta’addanci ne.

kakakin rundunar ‘yansandan kasar Anders Thornberg ya gayawa taron manema labarai yau lahadi cewa ana binciken harin a matsayin ta’addanci karkashin dokokin da kasar ta tanada kan haka, duk da haka hukumomi basu tsananta matakan tsaro cikin kasar ba.

‘Yansanda sunce harin na farko jiya Asabar ya auku ne ciki wata motakusa da wani titi da ake hada haddar cinikayya, ya raunata mutane biyu amma ba sosai ba. Jim kadan bayan fashewar farkon sai kuma aka ji ta biyu akan wan nan titin dai,daga bisani ‘yansanda suka sami gawar mutu daya a wurin. Hukumomi sun hakikance gawar ta dan kunar bakin wake ne.

Kamfanin dillancin labarai ta kasar TT ta bada labarin samun sakon email minti cikin harshen larabci da ta kasar,minti 10 kamin fashewar,sakon yana gargadin daukar mataki da ba’a bayyana ba. Haka kuma kamfanin dillancin labaran yace an kuma aike da wan nan sako ga rundunar ‘Yansanda,inda aka tabo batun sojojin Sweden a Afghanistan, da kuma zanen siffar Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, da wani mai zane dan kasar Sweden,mai suna Lars Vilks, ya yi.

XS
SM
MD
LG