Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Kunar Bakin Wake A Pakistan Ya Halaka Fiyeda Mutane 40.

Hoton wani da ya jikkata aharin kunar bakin wake da aka kai a Pakistan.

‘Yansanda a Pakistan sunce wani harin kunar bakin wake da aka kai yau Asabar a arewa maso yammacin kasar ya kashe akalla mutane 41 ya jikkata wasu da dama.

‘Yansanda a Pakistan sunce wani harin kunar bakin wake da aka kai yau Asabar a arewa maso yammacin kasar ya kashe akalla mutane 41 ya jikkata wasu da dama.

An kai harin ne a gundumar Bajur a sansani raba abinci ta hukumar wadata abinci ta Duniya,wacce take tallafawa mutane da fitinu suka raba da muahllansu.

Jami’ai sukace maharin yana sanye irin hijabi da ake kira Burqa,amma akwai rahotanni masu sabani da suke cewa maharar mace ce, ko dai na miji da ya yi shigar mata.

Gundumar tana kusa da kan iyakar kasar da Afghanistan,yanki da jami’an Amurka suka ce tungar mayakan sakan Taliban d a al-Qaida ne.

XS
SM
MD
LG