Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Venezuela Su Na Jayayyar Diflomasiya Akan Sabon Jakada


Shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez ya na kalubalantar Amurka cewa idan ta isa ta yanke huldar jakadanci da kasar shi.
Shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez ya na kalubalantar Amurka cewa idan ta isa ta yanke huldar jakadanci da kasar shi.

Amurka-Ta-Kwace-Bizar-Jakadan-Venezuela.

Amurka ta kwace bizar jakadan kasar Venezuela da ke nan birnin Washington D.C, Bernardo Alvarez, a cikin wani abu mai kama da ramuwar gayya ga matakin da gwamnatin kasar Venezuelar ta dauka, na kin amincewa da wanda Amurka ke son nadawa jakadan ta a kasar ta Venezuela.

Kakakin ma’aikatar harakokin wajen Amurka, Mark Toner, ya fada cewa, akwai sakamakon da ka iya biyo baya, saboda gwamnatin kasar Venezuela ta ki yarda Larry Palmer ya yiwa Amurka jakada a birnin Caracas. Amma kakaki Mark Toner ya ki ya kwance kulli, da aka nemi sanin ko wadanne irin abubuwa ne ka iya biyo baya.

Haka kuma Toner ya ce ci gaba da yin huldar diflomasiya da Venezuela, na da amfani ga kasar Amurka. Toner ya yi wannan furuci ne bayan da shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez, ya kalubalanci Amurka da cewa idan ta isa, ta katse huldar diflomasiya da ita saboda jayayyar da suke yi a kan sabon jakadan na Amurka.

Wasu ‘yan watanni da dama kenan dai da Amurka ke son tura Larry Palmer ya yi ma ta jakada a kasar Venezuela.To sai dai gwamnatin kasar ta Venezuela ta yi korafi game da wasu kalaman da shi Palmer ya taba yi cewa, sojojin kasar Venezuela ba su da isasshiyar da’a kuma ya ce gwamnatin kasar Venezuelar na da dangantaka da ‘yan tawayen kasar Colombia masu akidar gurguzu. Saboda haka ne shugaba Chavez ya ce dole ne duk wanda za shi kasar Venezuela da sunan jakadanci ya girmama ta.

XS
SM
MD
LG