Manyan abokan gaban Amurka din biyu, sun yi ta amfani da firgitar da Pakistan ke yi game da Indiya, da kuma gibin da Amurka ta bari na jagoranci a duniya, a yayin da Shugaba Trump ke cigaba da tsara irin nasa salon Shugabancin a wannan yanki mai muhimmanci.
Dangantakar Pakistan da hudu daga cikin makwabatanta - wata da Afghanistan da Indiya da Iran -- ta yi tsami. Kuma a maimakon ta dau matakan dakile tsattsauran ra'ayi, ga dukkan alamu gwamnatin na biye ma masu tsattsauran ra'ayin ne ta yadda babu ma alamar za ta soke dokar nan sabon addini da ake takaddama akai, wadda ta yi ta janyo tashin hankali.
Kwararru sun ce 13 daga cikin kungiyoyi 60 da Amurka ta ayyana a matsayin na ta'addanci a duniya a kasar Pakistan ne su ke, akasari a yankunan da ke karkashin ikon Kabilun da ke daura da iyakar Afghanistan.
Facebook Forum