Shugaban kasar Peru yace watakila kafin karshen shekarar nan gwamnati zata tsaida shawara a kan ko za a bayar da ahuwa bisa dalilai na rashin lafiya ga tsohon shugaba Alberto Fujimori dake daure a gidan kurkuku.
Shugaba Pedro Pablo Kuczynski, ya fadawa wani gidan rediyo na kasar jiya jumma’a cewa duk wata ahuwar da za a yi ma tsohon shugaban, ba wai ahuwa ce ta yafe masa laifuffukan da ya aikata ba, ahuwa ce da za a yi bisa irin shawarwarin da likitocin Mr. Fujimori zasu kawo.
Jiya jumma’a aka garzaya da tsohon shugaban asibiti a bayan abibda likitansa ya bayyana a zaman hawan jinni da bugun zuciya ba daidai ba.
Fujimori mai shekaru 78 da haihuwa yana zaman daurin shekaru 25 a kurkuku dangane da laifuffukan keta hakkin bil Adama, zarmiya da kuma kafa kungiyoyin ‘yan ina da kisa a lokacin da yake shugabancin kasar.
‘Yan zanga zanga sun fantsama a kan titunan Lima, babban birnin kasar jiya jumma’a domin shawo kan shugaba Kuczynski a kan kada ya yarda ya yi ma Mr. Fujimori ahuwa. An sha kai tsohon shugaban zuwa asibiti bisa laulayi iri iri tun lokacin da aka daure shi a kurkuku.
Facebook Forum