Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Papa Roma Francis Zai Kai Ziyara Sansanin 'Yan Gudun Hijira Na Falasdinawa Lahadin Nan.


Papa Roma Francis lokacinda yake barin kasar Jordan.
A ci gaba da rangadi na kwanaki uku da ya kai gabas ta tsakiya, yau lahadi ake sa ran Papa Roma Francis zai ziyarci wani sansanin ‘yan gudun hijira na Falasdinawa dake garin Bethelehem kusa da yammacin kogin Jordan, a ziyarar da zummar ta itace karfafa guiwar a cimma zaman lafiya a yankin.

Wani kakakin fadar Vatican yace Papa Roma zai yi amfani da wanan ziyara wajen bayyana matsayar cocin kan rikicin Isra’la da Falasdinawa da ya hada da ‘yancin Isra’ila na ci gaba da kasancewa cikin lumana da tsaro, da kuma hakin Falasdinawa na samun kasarsu mai diyauci.
XS
SM
MD
LG