Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paparoma Benedict ya shawarci 'yan Afirka su kauce wa tsarin kasuwanci mai cutarwa


Matasa na marabtar Paparoma Benedict a kasar Benin
Matasa na marabtar Paparoma Benedict a kasar Benin

Paparoma Benedict ya yi kira ga ‘yan Afirka da su yi watsi

Paparoma Benedict ya yi kira ga ‘yan Afirka da su yi watsi da abin da ya kira tsarin kasuwanci mai cutarwa, a yayin da nahiyar ke kokarin dacewa da zamani.

Paparoman ya isa babbar cibiyar kasuwancin kasar Benin wato Cotonou a jiya Jumma’a, inda dubban mutane su ka marabce shi. Mata da dama sun saka tufafe masu dauke da hoton fuskar Paparoman. Wasu mutanen ma kuka su ka rinka yi yayin da aka wuce da shugaban ‘yan Katolikan mai shekaru 84 cikin motarsa zuwa babbar Majami’ar birnin.

Da zuwansa, Paparoman yay i jawabi ne kan bukatar kasashen Afirka su dace da zamani, to amman sai yay i gargadi game da illar yinkurin dacewa da zamanin. Ya yi kira ga ‘yan Afirka da su kauce wa abinda ya kira mika wuya haka kawai ga tsare-tsaren harkokin kasuwancin zamani da na hada-hadar kudi.

Ya kuma yi gargadin cewa kabilanci da fifita kasa bisa wata da kuma rikicin addini na da hadarin gaske. Ya yi kira ga ‘yan Afirka da su mutunta kowane mutum da kowane iyali da kuma kowace halitta.

Babban musabbabin ziyarar da kwana uku shi ne gabatar da manufofin darikar ta Katolika game da nahiyar ta Afirka, inda nan ne mabiya darikar Katolika su ka fi karuwa a fadin duniya.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG