Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paparoma Francis Zai Yiwa Taron Majalisar Dinkin Duniya Jawabi Yau


Paparoma Francis da jama'a

Bayan kwanaki uku da ya yi yana ziyara a Washington DC fadar gwamnatin Amurka kuma cibiyar siyasar duniya yanzu Paparoma Francis ya mayarda hankalinsa zuwa cibiyar kasuwanci ta duniya wato Newa York.

Paparoma Francis dan shekaru 78 da haihuwa ya bar Washington DC jiya zuwa birnin New York inda zai cigaba da ziyararsa.

Yau Juma'a Paparoman zai yiwa shugabannin kasashen duniya da suke taron Majalisar Dinkin Duniya jawabi. Bayan jawabinsa zai wuce zuwa wurin dogayen gine ginen nan biyu na cibiyar kasuwanci da 'yan ta'ada suka kai ma hari ranar 11 ga watan Satumbar 2001 inda za'a yi sujadar hadin gwiwar duk addinai.

Bayan ya ziyarci wata makarantar firamare ta Katolika dake gabashin anguwar Harlem inda bakake da spaniyawa suka fi yawa Paparoma zai yi sujada a Madison Square Garden da yamma. Ana kayautata zato mutane fiye da 20,000 zasu kasance a wurin sujadar.

Ranar Asabar Paparoma zai tafi Philadelphia dake jihar Pennsylvania inda zai yi kwana biyu kafin ya bar Amurka. A Phildelphia ne zai halarci taron iyalai na duniya da darikar Katolika ta shirya. Ranar Lahadi kuma zai yi sujada wadda zata tattaro mutane kimanin miliyan biyu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG