Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paparoma Francis ya Fara Ziyarar Mako Daya Zuwa Kasashen Asiya


Paparoma.
Paparoma.

Paparoma Francis ya fara ziyarar mako daya zuwa kasashen Asiya. Ya bar Rome zuwa Sri Lanka daga nan kuma ya wuce Philipines.

Karo na biyu ke nan da Paparoman zai kai ziyara nahiyar Asiya lamarin da ake ganin yana cikin shirin cocin na kai bishara kasashe masu tasowa.
Paparoma zai isa Sri Lanka yau Talata inda zai soma da jawabi akan hadin kan addinan kasar da har yanzu bata murmure ba daga yakin basasa da tayi fama dashi.

Sabon Shugaban kasar Maithripala Sirisena, wanda ya ci zaben bazata makon jiya, shi ne zai karbi bakuncin sa Tun farko sabon shugaban yayi alkawarin mutunta duk addinan kasar musamman na tsirarun jisuna.
Mabiya addinin Bhuda suka fi yawa a kasar Sri Lanka amma darikar Katolika na ganin kanta a matsayin wadda take kawo hadin kai cikin al’ummomin kasar domin tana da mabiya daga kabilar Sinhalese da ta fi yawa da kuma tsirarun Tamil.

Yawancin Sinhalese addinin Budha su keyi yayin da kuma Tamil sun fi yawa a addinin Hindu.

Ranar Alhamis Paparoma zai tafi kasar Philipins kasar da tafi kowace kasa yawan ‘yan darikar Katolika a duk fadin nahiyar Asiya. Ana zaton miliyoyin mabiya darikar zasu halarci sujadar da Paparoma Francis zai yi a wani katafaren fili.

XS
SM
MD
LG