Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Ta Ce Sai Jam’iyar APC Ta Tsayar da Buhari Dan Takarar Ta Zata Maida Martani


PDP logo

Game da batun tsayawa takararsa a zaben shekarar 2019, yanzu haka babbar jam’iyar adawa ta PDP a Najeriya ta maida martani inda tace akwai tufka da warwara, saboda shi dai Shugaba Buhari ya sanar da cewa zai tsaya takarar ne bayan da aka shafe watanni anata cece-kuce na ko zai sake tsayawa ko kuma a'a.

Babbar jam'iyyar adawar ta PDP, dai ta ce za ta maida martani ne bayan Muhammadu Buhari ya samu tikiti jam'iyyar APC na tsayawa takarar zaben, ba wai kawai don yace zai cigaba ba.

Jam’iyar ta bakin mai magana da yawun shugaban jam'iyyar ta PDP a Najeriya Shehu Yusuf Kura yace jam'iyyar su bata fargabar tsayawa takarar Muhammadu Buhari, domin a cewarsa ai jiki magayi.

Haka nan kuma jam’iyar ta soki batun sunayen da aka fitar na yayan jam’iyark ta PDP da ake zargin su suka washe kudaden Najeriya.

To sai dai yayin da PDP ke zargin yan kasa na wahala tuni wasu yan gani kashen Buhari suka soma gangami a jihohi don tallata gwaninsu, kamar yadda Yakubu Gwamna da wasu kusoshin APC suka jagoranci wani gangami a Jalingo, fadar jihar Taraba.

Tuni dai Shugaba Buhari ya sanar da cewa zai tsaya takarar bayan da aka shafe watanni anata tababar ko zai sake tsayawa ko kuma a'a.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG