Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar PDP Ta Ce Ba Ta Ganin Buhari a Matsayin Dan Takara


Babban taron jam'iyyar adawa ta PDP na kasa

Jam,iyyar PDP ta ce sanarwar da Buhari ya bayar ta cewa zai tsaya takara a shekarar 2019 matsalar jam’iyyar APC ce ta cikin gida, domin har yanzu APC ba ta tsayar da shi a matsayin dan takara ba.

A wata sanarwa da jam’iyyar PDP ta wallafa a shafinta na Facebook akan yanar gizo, ta bayyana cewa sanarwar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, harka ce ta cikin gida.

Sanarwar wacce ke dauke da sa hannun Sakataren Yada Labaran jam'iyar ta PDP, Kola Ologbondiyan, ta ce har yanzu Buhari bai zama dan takara ba.

Fitowar da Buhari ya yi, ya bayyana aniyarsa a jiya Litinin, ta sanya shi a matsayin dan takarar neman shugabancin Najeriya a zabe mai zuwa, wanda za a gudanar a watan Mayun shekarar 2019.

"Sai APC ta tsayar da shi a matsayin dan takara, amma a yanzu ba za mu bata lokacinmu, don kawai ya ce zai tsaya takara ba." a cewar PDP.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG