Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Ta Kira INEC Ta Soke Zaben Majalisar Wakilai Na Jeri Borno


미국 뉴욕 센트럴파크웨스트에서 진행된 제90회 메이시스 추수감사절 퍼레이드에 선보인 대형 패딩턴 베어 풍선.<br /> &nbsp;

PDP na son INEC ta soke zaben dan majalisar wakilan tarayya da aka ji a karamar hukumar Jeri dake jihar Borno

Magoya bayan jam'iyyar PDP sun koka da zaben sabili da wasu kurakurai da dama akan yadda aka gudanar da zaben..

Mutanen suna zargin akwai rashin kwarewa da kuma hada baki da aka yi da wasu malaman zaben.

Alhaji Yunus Mongunu shi ya kira taron manema labarai a madadain PDP a garin Maiduguri. Yace sun kira INEC ta soke zaben domin a samu zaman lafiya kana mutanen da aka hanasu yin zabe su samu su yi.

Idan INEC bata yi hakan ba zasu garzaya kotu domin sun mika kokensu a rubuce. Yace ba'a yi anfani da naura ba kuma takardar da ta kamata a cika ba'a cika ba.

A wani halin kuma wani dattijo da ya fito daga Damboa dake jihar Borno ya koka ne kan irin matsalolin da suka fada. Yace sukan kwashe awanni da dama kafin su isa garin Damboan duk da cewa mafi yawansu suna gudun hijira a cikin Maiduguri. T

Yace daga Maiduguri zuwa Damboa babu hanya. Sai da suka yi tafiyar kilomita 800 kafin su isa Damboa.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG