Accessibility links

ZABEN 2015: Za'a Yi Anfani da Naura a Zabe Mai Zuwa-inji INEC


Shugaban Hukumar Zabe ta INEC Farfasa Attahiru Jega

Hukumar zabe ta INEC ta kara jaddada matsayinta cewa ba gudu ba ja da baya tilas ne za'a yi anfani da naura mai tantance masu jefa kuir'a a zabe mai zuwa.

Za'a yi anfani da naurar ne a zaben gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi da za'a yi ranar Asabar mai zuwa, wato ranar 11 ga wannan watan a duk fadin kasar Najeriya.

Wakazalika hukumar ta bada umurni ga duka wakilanta na jihohi cewa su tabbatar an bi ka'ida da dokokin dake rubuce a tsare-tsaren da za'a yi anfani dasu a zaben.

Hajiya Amina Zakari daya daga cikin kwamishanonin zabe ta bada amsa akan mahimman abubuwa da suka jibanci zaben. Tace babu banbanci da zaben shugaban kasa inda suka bari aka yi anfani da rubuta sunaye a wuraren da naura bata yi aiki ba. Amma a zabe mai zuwa sai an tantace mutum da naurar. Idan bata yi aiki ba ranar zaben to sai a dawo washegari a yi zabe. Matsalar da aka samu da naurar ta samu asali ne saboda rashin yi mata caji sosai kafin a raba a kaisu wurin zabe. A wasu wuraren rashin hakurin jama'a ya sa aka kasa yin anfani da ita. A wasu wuraren kuma ba wadanda suka samu horo akan yin anfani da naurar ba ne suka je runfunan zabe.

Ga rahoton Umar Faruk Musa.

XS
SM
MD
LG