Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Ta Nemi Kotu Ta Cire Mai Mala Buni Daga Mukamin Gwamnan Yobe


Shugaban Jam'iyyar PDP, Uche Secondus.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta shigar da karar jam’iyyar APC mai mulki da Mai Mala Buni a gaban kotu, tana neman a ta cire shi daga kujerarsa ta gwamnan jihar Yobe.

Lauyan PDP, Emeka Etiaba ne ya shigar da wannan kara a cikin wata takardar sammaci mai shafi hudu da ya gabatar a gaban babbar kotun a ranar Alhamis kamar yadda gidan talabijan na Channels ya bayyana.

Jam'iyyar ta PDP ta bukaci kotun da ta baiwa gwamna Buni sammaci don ya bayyana a gabanta, tare da ba da hujojjin kare kansa a kan ko ya cancanta ya ci gaba da rike mukamin gwamna ko akasin haka bayan amincewarsa da karabar mukamin shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC mai mulkin kasar.

A cewar jam’iyyar PDP, gwamna Buni ya sabawa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya sashe na 183, domin yana matsayinsa na gwamna mai cikakken iko, ya kuma rike mukamin shugaban riko na jam’iyya APC na kasa.

Ko bayan jam’iyyar PDP, akwai wasu masu shigar da karar da ke gaban babbar kotun tarayyar mai lamba FHC/ABJ/CS/885/2021.

Sun hada da tsohon dan takarar gwamnan jihar Yobe karkashin inuwar jam’iyyar PDP a shekarar 2019, Umar Iliya Damagum, da abokin takarar sa, Abba Abba Aji.

Wadanda jam’iyyar PDP ke kara kuwa ban da gwamna Buni, akwai mataimakinsa, Idi Barde Gubana, jam’iyyar APC, da kuma hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya wato INEC.

Idan ana iya tunawa dai shigar da karar da jam’iyyar adawa ta PDP ta yi na zuwa ne bayan hukuncin kotun koli a shari’ar da ke tsakanin gwamnan Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, da mista Eyitayo Jegede, tsohon dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan Ondo na shekarar 2020.

A baya PDP da tsohon dan takarar ta Jegede sun nemi Kotun daukaka kara da ke birnin Akure da ta kori gwamna Akeredolu daga kijerar gwamna ne bisa hujjar cewa gwamna Buni, wanda kuma ke matsayin shugaban kwamitin rikon kwarya na APC da ya sanya hannu kan takardar tsayawa takararsa a matsayin gwamna mai ci a halin yanzu ya sabawa doka.

Hukuncin kotun koli da ya tabbatar da zaben gwamna Akeredolu da amincewar masu shari’a hudu, yayin wasu uku suka kalubalanci zaman Buni a matsayin shugaban kwamitin riko na APC dai ya bar baya da kura.

To sai dai kuma a wani hukuncin baya-bayan nan, kotun kolin kasar ta warware wannan takaddama, inda ta ce gwamna Mai Mala Buni bai karya doka ba don rike mukamin shugabancin jam'iyyar APC na rikon kwarya.

A nata martani ta bakin kakakin ta, James Akpanudoedehe , jam'iyyar APC ta bukaci jam'iyyar adawa ta PDP ta mayar da hankali kan barakar da ke cikin gidanta a maimakon tsoma baki kan lamarin da bai shafe ta ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG