Accessibility links

PDP ta Rubutawa Kakakin Majalisar Wakilai ya Kori Wadanda Suka Canza Sheka.


Kakaki Aminu Waziri Tambuwal

Bayan da wasu 'yan majalisar wakilai 37 daga jam'iyyar PDP suka canza sheka zuwa jam'iyyar adawa ta APC jam'iyyar ta bukaci kakakin majalisar ya koresu.

Kwana biyu bayan da wasu 'yan jam'iyyar PDP a majalisar wakilai suka canza sheka, jam'iyyar ta bukaci a koresu daga kujerunsu.

A wasikar da PDP ta rubutawa kakakin majalisar Aminu Waziri Tambuwal wadda ta samu sa hannun sakataren labarun jam'iyyar Olise Metuh ya ce 'yan majalisar 37 da suka canza sheka sun sadakar da kujerunsu don haka kakakin ya koresu. A bisa tsarin kundun mulki na 1999 'yan majalisar sun sayar da kujerunsu. Alhasan Ado Doguwa na cikin wadanda suka canz sheka zuwa APC ya yi watsi da barazanar. Ya ce yau ne PDP ta san kakakin majalisar nada ikon da zai iya yin wani abu. Ya ce kwana kwanan nan majalisun biyu suka samu ministar ma'aikatar zirga zirgan jiragen sama Stella Oduah da hannu dumu-dumu wurin cin amanar kasar kuma suka fada ma shugaban kasa ya koreta amma ya yi masu kunnen shegu. Har yanzu PDP ta rike matar da ta yi badakala da kudin jama'a cikin gwamnati.

A gefe guda shugaban matasan PDP na Yobe Ado Adamu Bomboy ya yaba da matsayin hukumar zabe Farfasa Attahiru Jega kan yiwuwar dakatar da zaben 2015 a jihohin Adamawa da Borno da Yobe. Ya ce an kashe mutane da 'yan makaranta an yi barna kana kuma a ce mutane su zo su shga zabe. Ya ce basu damu da mutane ba, shugabanci ne ya damesu. Ya ce a nashi ra'ayi Jega ya yi daidai Allah ya bashi ikon yin hakan. Kada a barsu su yi zabe sai sun aiwatar da zaman lafiya tukunna, matasa sun samu abun yi, hanyoyi an gyara, an kawo ruwan sha da wutar lantarki kana a tabbatar jihohin sun koma kamar kowace jiha sa'an nan a shirya zabe.

Yanzu dai gwamnonin PDP sun kirawo wani taron gaggawa.

Ga rahoton Saleh Ashaka.

XS
SM
MD
LG