Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Ta Sha Kayi a Jihar Adamawa


PDP

Bayan lashe kananan hukumomi 14 cikin 21 dan takarar jam'iyyar APC ya lashe kujerar gwamnan Adamawa.

Sanata Bindoji Birlo na jam'iyyar APC shi ne ya lashe kujerar gwamnan jihar Adamawa.

Bindoji ya doke tsohon shugaban hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC Malam Nuhu Ribadu na jam'iyyar PDP.

Tun kafin a kammala sakamakon zaben Malam Nuhu Ribadu ya fitar da wata sanarwa inda ya rungumi kadara da sakamakon zaben, ya amince ya sha kayi. Sauran 'yan takaran su ma sun ce duk yanayin da mutum ya samu kansa ya godewa Allah. Sun ji dadi an yi zaben lafiya an kuma gama lafiya.Sun yiwa gwamnatin dake shigowa fatan alheri da kuma kira a yi gaskiya da adalci. A rike kowa a yi tafiya tare.

Su ma 'yan jam'iyyar APC a jihar sun yi murna. Suna yiwa Allah godiya domin shi ne ya kawo.

Amma a jihar Taraba APC ta ki ta amince da sakamakon zaben wasu kananan hukumomi nda take zargin an yi magudi.

Ga rahoton Ibrahi Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:51 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG