Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pentagon Tace Bata Da Wani Bayani Na Mutuwar Shugaban Kungiyar Daesh (ISIS)


Abu Bakr al-Baghdadi

Duk da bayanin da kungiyar rajin kare bil adama ta Syria tayi na mutuwar Abu Bakr Al-Baghdadi, Helkwatar sojin Amurka ta ce ba ta da wani bayani akai.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon tace ba ta da wani bayani dake nuna cewa madugun kungiyar ISIS, Abu Bakr al-Baghdadi ya mutu.

Wannan bayanin ya biyo ne bayan rahoton da kungiyar ‘yan rajin kare hakkin bil adama ta Syria da ake ira “Observatory”, wacce mazauninta ke a Ingila, ta bayar ne, cewa shugaban IS din ya mutu.

Wani darektan kungiyar, Rami Abdel Rahman ya gayawa kampanin dillacin labarai na AP cewa a yau ne aka sanar da su gameda rasuwar al-Baghdadi.

Shi dai al-Baghdadi, wanda tun shekarar 2014 ya kaddamar da abinda ya kira Daular IS,” an sha bada rahoton mutuwarsa ko ji mishi rauni tun daga lokacinda ya dauki ragamar shugabancin kungiyar ta shekaru ukku da suka wuce.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG