Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Peugeot Na Shirin Samarwa Ma'aikatan Najeriya Motoci


Tambarin Peugeot
Tambarin Peugeot

Kamfanin hada motocin Peugeot dake zama kamfanin hada motoci na farko a Najeriya, ya ce yana wani shiri da gwamnatin Kasar na ganin yan Najeriya musanman ma'aikata sun mallaki sababbin motocin hawa da nufin rage hatsura da ake alakantawa da motocin Takunbo.

Abin tambaya anan shine anya yarjeniyar da Najeriya ta cimma da kasar China bazata kawo cikas ga harkokin kasuwancin kamfanin ba. Tambayar kenan da Wakilinmu Babangida Jibril ya yiwa Manajan Kasuwanci na Kanfanin Alhaji Sulaiman Sulaiman, mai kula da shiyar Lagos a wajen bikin baje kolin motoci na Lagos, koda yake da farko yayi bayani ne akan hanyoyin mallakar motocin ga yan Najeriya.

Inda yace ganin yanayin yadda kasa take ne yasa suka hada hannu da wasu bankuna domin ma’aikata suje a yi musu bayanin abinda ake bukata kafin su sami sabuwar mota, domin duk wanda albashinsa yakai Naira Dubu 100 to tabbas zai iya samun sabuwar mota.

Duk da yake akwai kamfanoni dayawa da ake zuwa daga waje ana kafawa a Najeriya, duk da haka Alhaji Sulaiman yace kamfanin Peugeot baya fargabar komai domin sauran kamfanoni ba zasu iya zama kalubale ba garesu.

Saurari hira da manajan kasuwancin Peugeot Alhaji Sulaiman.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:59 0:00

XS
SM
MD
LG